Al-Bashir ya ce, kasarsa ta tsara wani shiri da aminansu, kuma abokansu na kasar Rasha, domin zamanantar da rundunar sojojin kasar dake yankin tekun Red Sea.
Ya kara da cewa, sun tanadi wani cikakken tsari na kafa rundunar soji mai karfi ta fuskoki uku da suka hada da jami'ai, kayan aiki, da yanayin muhallin aikin.
Shugaban na Sudan ya cigaba da cewa, a shekarun baya sun dogara ne kacokan wajen shigo da dukkan kayayyakin aikin soji daga kasashen ketare, hatta albarusai da suke amfani da su, amma a halin yanzu, suna iya kera kananan bindigogi har ma da manyan makamai, da jirgin saman yaki da kuma jirgin ruwan yaki a cikin kasar. (Ahmad)