in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta sake nada tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar
2018-02-12 11:53:40 cri

A ranar Lahadi kasar Sudan ta sake nada Salah Abdallah Gosh, a matsayin shugaban hukumar leken asirin kasar (NISS), bayan ya shafe shekaru 9 yana hutu.

Shi dai Gosh, ya taba zama babban jami'in hukumar ta NISS tsakanin shekarun 1999-2009, inda a wancan lokacin ya taimaka wajen karfafa kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin hukumar ta NISS da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Amurka.

Ya taba zama mashawarci ga shugaban kasar bayan da ya bar hukumar ta NISS, har zuwa farkon shekarar 2011, inda aka sauke shi daga kan mukaminsa.

A watan Nuwamba shekarar 2012, Gosh an zarge shi da hannu a yunkurin juyin mulkin sojoji, kafin daga bisani aka sake shi a karkashin shirin afuwa na ofishin shugaban kasa a shekarar 2013.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China