An kai hari wani sansanin soja dake kudu maso yammacin kasar Kamaru
2017-12-19 16:06:42
cri
Wani jami'in hukumar tsaro a kasar Kamaru ya bayyana a jiya Litinin cewa, an kai hari wani sansanin soja dake kudu maso yammacin kasar da ke dab da iyakar kasar da Nijeriya, kuma harin ya haddasa mutuwar sojoji 4. Ana dai zargi 'yan aware dake yankin da ake magana da harshen Turanci na kasar Kamaru da kai harin. (Zainab)