in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun mutu a sanadiyyar harin Boko Haram a yankin arewa mai nisa a Kamaru
2017-12-13 11:05:44 cri
Kimanin mutune biyu ciki har da farar hula guda ne aka kashe a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta kaddamar a daren ranar Talata a yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru, wata majiya ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua afkuwar lamarin.

A cewar wani mazaunin yankin, an kaddamar da harin ne da misalin karfe 7 zuwa 8 na dare agogon yankin, wanda yayi dai dai karfe 8 zuwa 9 agogon GMT a ofishin 'yan sanda na Mayo-Sava dake garin Amchide, wanda ke makwabtaka da Najeriya.

Maharin bam din ya hallaka wani mutumin kauye, a lokacin da maharin yayi amfani da yanayi na duhun dare wajen kaddamar da harin a lokacin da mutane ke kokarin halartar salla.

Ofishin 'yan sanda na Mayo-Sava ya fuskanci hasarar rayuka har na mutane 6, wanda ke da nasaba da Boko Haram daga ranar Litinin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China