in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta damu game da yawan mata da kananan yara dake kaura daga jamhuriyar Kamaru
2018-01-20 12:08:51 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta bayyana damuwarta game da matsanancin halin da mata da kananan yara ke fuskanta a yankunan dake magana da yaren Turanci a jamhuriyar Kamaru, lamarin da ya tilasta su tserewa zuwa Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR, William Spindler, ya fadawa manema labarai jiya Jumma'a cewa, daga cikin adadin 'yan gudun hijirar su 10,000, kashi 80 bisa 100 mata ne da kananan yara, wadanda tuni aka yi musu rajista a jihar Cross River dake gabashin Najeriyar.

Akwai kuma dubban 'yan kasar Kamarun a wasu jahohin dake makwabtaka, wadanda ba'a yi musu rajistar ba, kuma kashi 50 bisa 100 na adadin kananan yara ne, wadanda suka tsere daga yankunan da masu magana da yaren Faransanci suke da rinjaye.

Spindler ya ce, yaran da ba su karkashin kulawar kowa da kuma wadanda suka rabu da iyayensu su ne suka fi shiga matsanancin halin rayuwa, musamman na rashin samun damar karbar tallafin abinci da sauran kayayyakin jin kai. Hukumar UNHCR ta samu labarin cewa mafi yawa daga cikin yaran sun dogara ne wajen yin aikin karfi ko kuma yin barace barace don samun dan abin da za su kai bakinsu, ko kuma su taimakawa danginsu.

UNHCR ta ce tana aiki da mahukuntan Najeriya don sake hada yaran da suka rabu da iyayensu a wuri guda da kuma ba su kariya da ba su abu mafi muhimmanci wato ilmi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China