in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya bukaci a tattauna hanyoyin magance rikicin kudancin Kamaru
2018-01-24 11:12:09 cri
Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya bukaci a yi amfani da hanyoyin tattaunawa a matsayin hanyar da zata kawo karshen rikicin da ya dabaibaye yankin kudancin jamhuriyar Kamaru, lamarin da ya tilasta mazauna yankin yin hjijra zuwa Najeriya.

Mbasogo, yayi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja, fadar mulkin kasar, yace babu wata kasa a duniya da bata da wani kalubale na musamman dake damunta.

A halin yanzu tashin hankali ya barke a Kamaru. Dubban mutane dake yankuna masu magana da yaren Turanci sun tsere daga yankunan sakamakon barkewar tashin hankalin, kuma da dama daga cikinsu suna ta yin kiraye kirayen neman a basu kasarsu mai cin gashin kai.

Shugaban kasar wanda ke ziyarar aiki a Najeriyar ya shedawa 'yan jaridu cewa, abinda kawai zai kawo karshen rikicin shine dukkannin bangarorin da abin ya shafa su hada kai don zama a teburin sulhu da nufin tattauna matakan da zasu warware matsalar.

Shugaban ya yabawa kokarin da shugaba Buhari keyi na yakar kungiyar Boko Haram, ya kara da cewa, shugaban Najeriya yana yin namijin kokari na yakar ayyukan 'yan tada kayar baya a ciki da wajen Najeriyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China