Shugaban na Sin ya yi kiran ne ga mambobin JKS, yana mai fatan za su ci gaba da bada gudunmawa wajen ciyar da kasar gaba, da bunkasa tattalin arzikin ta ta yadda zai zamo mai cike da karsashi da kyakkyawar makoma.
Ya ce sai da tattalin arziki na zamani ne kasar Sin za ta yi kafada da kafada da zamani, ta kuma shiga gogayya da sauran kasashen duniya, tare da samar da tallafi ga ci gaban sauran sassa na zamanantar da harkoki.