in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin: Sassa masu zama kansu suna da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki
2018-01-22 19:06:48 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, a cikin shekaru arba'in da suka gabata sassa masu zaman kansu na kasar sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki, yayata harkokin kirkire-kirkire, samar da guraben ayyukan yi, da inganta rayuwar al'umma.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Litinin din nan a cikin sakon taya murna da ya aike wa babban taron sassa masu zaman kansu karo na biyar. Ya ce tun lokacin da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje shekaru arba'in da suka gabata, sassa masu zaman kansu na kasar suka kara samun ci gaba, kana sashen ya kasance wani muhimmin bangare na tattalin arzikin kasar.

Bayanai na cewa, a karshen shekarar 2017, akwai kimanin mutane miliyan 65.79 dake gudanar da harkokin kasuwanci na kashin kansu baya ga sama da kamfanoni miliyan 27.26 masu zaman kansu wadanda suka samarwa mutane miliyan 341 guraben aikin yi.

Shugaba Xi ya ce ya kamata kamfanoni da 'yan kasuwa masu zamansu su bunkasa harkokin masana'antu, tafiyar da harkokin tattalin arzikin yadda ya kamata tare da samar da ci gaba mai inganci. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China