A cewar ma'aikatar cinikayyar kasar ta Sin, a shekarar 2017 da ta gabata, kudaden cinikayyar yanar gizo a yankunan karkarar kasar ya kai Yuan tiriliyan 1.24, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 194.1, karuwar kaso 39.1 cikin 100 bisa shekarar da ta gabata ce.
Bugu da kari, a karshen shekarar 2017 din, sama da kantuna miliyan 9.8 dake cinikayya ta yanar gizo suna kauyuka ne, karuwar kaso 20.7 cikin 100 a kan shekarar 2016, sun kuma samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 28. (Ibrahim Yaya)