Mataimakin firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya umurci gwamnatin kasar sa da ta tsara wani shiri, domin taimakawa kamfannonin yawon shakatawa da suka ci karo da hasara a sakamakon daina zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasar Masar. Har ila yau, kawo yanzu ba a kai ga samun cikakken dalilin faduwar jirgin saman kasar ba tukuna.
A game da labarin da hukumomin leken asiri na kasashen Amurka da na Birtaniya suka bayar, cewa wai jirgin saman ya fadi ne a sakamakon fashewar boma-boman da aka sanya a cikin kayayyakin fasinjan jirgin sama, kwamitin bincike ya bayyana cewa, bai samu shaidu ko kadan da za su tabbatar da hakan ba.
Domin tabbatar da tsaro, kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Turkiya da kuma Saudiyya sun sanar da dakatar da saukar jiragen saman su a birnin Sharmel Sheikh na kasar Masar. Yayin da ita kuma Rasha ta soke sufurin dukkan jiragen saman ta zuwa kasar Masar tun daga ranar 6 ga wata. (Lami)