in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren Janar na MDD ya yi kira da a kwantar da hankalin al'ummar DRC dake zaman dar-dar domin gudanar da zabe
2016-12-22 11:09:43 cri

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya yi kira ga shugabannin siyasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC, da su yi kokarin kwantar da hankalin al'ummar kasar da ke zaune cikin fargaba, tare da samar da kyakyawan yanayin gudanar da zabe a kan lokaci.

Zanga-zanga ya barke a wasu wurare a kasar ciki har da Kinshasa, babban birnin kasar, sanadiyyar karewar wa'adin mulkin shugaba Joseph Kabila a ranar 19 ga watan nan da muke ciki, ba tare da an gudanar da zabe domin samun wanda zai maye gurbinsa ba.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sakatare Janar din ya fitar, Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da rahoton asarar rayuka da aka samu yayin arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, yana mai jadadda bukatar jami'an tsaro kasar su kasance masu taka-tsantsan da juriya, a lokacin da suke tabbatar da tsaron al'umma.

Sanarwar ta kuma ruwaito Sakatare Janar din, na yin kira ga dukkan 'yan siyasa, cikin har da bangaren adawa, da su rika taka-tsantsan a duk abun da suke yi, yana mai kira ga magoya bayansu kuma, da su kauracewa tada rikici. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China