in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta game da dokar tafiye-tafiye kan yankin Taiwan da Amurka ta fitar
2018-02-09 20:25:17 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana rashin jin dadinsu kan wata dokar tafiye-tafiye mai nasaba da yankn Taiwan da Amurka ta fitar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan Jumma'ar nan yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin ta nuna rashin amincewa matuka kan wannan doka, kuma ta nunawa Amurkar bacin ranta kan wannan mataki.

A cewarsa, manufar kasar Sin daya tak a duniya wani ginshikin siyasa ne na alakar dake tsakanin kasashen biyu. A don haka, kasar Sin tana kira ga bangaren Amurka da ya martaba batun yankin Taiwan, ya kuma dakatar da aiwatar da wannan doka, sannan ya daidaita batutuwan da suka shafi yankin Taiwan yadda ya kamata, ya kuma tabbatar da alakar Sin da Amurka da ma yanayin da ake a zirin Taiwan.

A ranar Laraba ne, kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dattawan Amurka ya amince da dokar tafiye-tafiye da ta shafi yankin Taiwan na kasar Sin, dokar da za ta baiwa manyan jami'an Amurka da yankin Taiwan damar kaiwa juna ziyara. A watan Janairu ne ita ma majalisar wakilan Amurkar ta amince da wannan doka,(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China