Rahotannin da muka samu sun ce, a cikin jawabin Donald Trump, ya ce kasashen Sin da Rasha abokan gogayya ne na kasar Amurka. Game da wannan furuci, Madam Hua ta ce, akwai babbar moriya kusan irin daya tsakanin Sin da Amurka, yayin da ake kuma samun wasu sabani na ra'ayi, amma moriyarsu ta fi sabanin. Ta ce tarihi ya shaida cewa, hadin-gwiwa ita ce hanya daya tilo madaidaiciya da ya kamata kasashen biyu su zaba, hakan kuma zai sa kasashen biyu su ci moriya tare, da samun makoma mai haske. (Murtala Zhang)