Mai magana da yawun rundunar sojan kasar Uganda Birgediya Richard Karemire shi ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Alhamis, yana mai cewa, horas da jami'an fasahar gina layin dogo na SGR wanda kamfanin CHEC na kasar Sin ya dauki nauyi ya baiwa injiniyoyi daga rundunar sojan kasar kwarewar gina layin dogo na SGR,wanda zai hade kasar ta Uganda da tashar jiragen ruwa ta Mombasa dake Kenya.
A watan Agustan shekarar da ta gabata ce kamfanin CHEC na kasar Sin da aka baiwa kwangilar gina layin dogo a Ugandan suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da rundunar sojan Ugandan, zai kuma horas da jami'an kasar game da wannan aiki.
Bugu da kari, kamfanin zai yi aiki da UPDF wajen gina makarantar kimiyya da fasaha a gudumar Tororo dake iyakar gabashin kasar.
Da zarar an kammala aikin gina layin dogon, za a kwashe kwanaki biyu ne kacal wajen jigilar kayayyaki daga Mombasa zuwa Kampala, babban birnin Uganda. Maimakon kwanaki 14 da ake dauka a baya, lamarin da zai rage kudaden da ake kashewa ba ya ga bunkasa tattalin arzikin kasar.(Ibrahim)