Manaja mai kula da aikin Kong Tao ya shaidawa manema labarai cewa, layin dogon wanda zai lakume dala miliyan 823 na da tsawon km 45 da kuma tashoshin daukar fasinja guda 12.
Hanyar za ta hada filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin, yana mai cewa hanyar za ta kasance tagwaye.
Kong Tao ya kara da cewa, babban aikin na tafiya ba tare da tangarda ba.
A cewarsa, za a yi gwaji cikin watan Nuwamba sannan a kaddamar domin amfanin al'umma a watan Decemba.
Ya ce bayan kammala aikin, zai samar da ayyukan yi da bunkasa harkokin kasuwancin tare da habaka ci gaban tatalin arzikin kasar.