in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar diflomasiyya ce babbar damar warware batun zirin Koriya, in ji ministan tsaron Amurka
2018-02-08 13:01:00 cri
Ministan harkokin tsaron kasar Amurka James Norman Mattis ya bayyana a jiya Laraba cewa, a halin yanzu, hanyar diflomasiyya ce kadai ke ci gaba da kasance muhimmiyar hanya ta warware batun zirin Koriya, kuma kasar Amurka tana ba da gudummawa game da wannan aiki.

Mr. Mattis ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka yi a fadar White House ta kasar Amurka. Ya ce Amurka ta karfafa manufofin ta game da warware batun zirin Koriya ta hanyar diflomasiyya, sa'an nan kuma, kwamitin sulhu na MDD zai fidda wasu kudurorin dake shafar wannan batun.

Bugu da kari, ya ce, gamayyar kasa da kasa suna ci gaba da cimma matsayi daya kan batun zirin Koriya, lamarin da ya nuna cewa, suna dukufa wajen warware batun ta hanyar diflomasiyya.

Haka zakila, bayan ganawarsa da firaministan kasar Japan Shinzo Abe a ranar 7 ga wata, mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Japan ya yi bayani cewa, kasarsa za ta kakabawa kasar Koriya ta Arewa takunkumi mafi tsanani a fannin tattalin arziki. Sa'an nan, za ta yi hadin gwiwa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, wajen ciyar da aikin kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya gaba.

Bisa labarin da aka samu, an ce, a ranar 9 ga wata, Mike Pence da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar ta Koriya ta Arewa Kim Yong-nam, dukkansu za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da za a yi a birnin Pyeongchang na Koriya ta Kudu, lamarin da ke karfafa tambayar ko shugabannin biyu za su yi shawarwari a tsakaninsu ko a'a.

Amma kafin tashin Mike Pence zuwa kasar Japan, ya bayyana wa kafofin watsa labaran kasar Amurka cewa, mai iyuwa ne, zai gana da shugabannin kasar Koriya ta Arewa a birnin Pyeongchang. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China