in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sanya hannu kan sabuwar dokar kakabawa Koriya ta arewa takunkumi
2017-09-22 09:53:15 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanya hannu kan wata doka da nufin kara zaftare adadin kudaden shigar da kasar Koriya ta arewa DPRK ke samu.

Da yake karin haske game da batun shirin gwajin makaman nukiliyar DPRK wanda ya bayyana shi a matsayin barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya, mista Trump ya shedawa 'yan jaridu cewa, sabuwar dokar da ya rattabawa hannu zata taimaka wajen rage adadin kudaden shigar da DPRK ke samu wadanda da su ne take aiwatar da shirinta na kera makaman nukiliyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China