in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tillerson: Amurka za ta iya tattaunawa da Koriya ta arewa
2017-12-13 09:43:37 cri

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce kasar sa na da burin tattaunawa da mahukuntan Koriya ta arewa ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Tillerson wanda ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki game da manufofin gudanarwar Amurka, ya kara da cewa, ana iya tattaunawar da zarar mahukuntan Pyongyang sun shirya.

Kalaman na sakataren harkokin wajen Amurka dai na zuwa ne yayin da ake kara fuskantar karuwar yanayi na zaman dardar a zirin koriya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China