in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka tsakanin kasar Sin da Burundi ta kasance mafi kyau a tarihi
2018-01-27 12:22:48 cri
Kakakin shugaban kasar Burundi ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Burundi ta kasance mafi kyau a tarihi, inda ya bukaci a kara kyautata cudanya da mu'amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

Jean Claude Ndenzako Karerwa, ya fada a yayin zantarwa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bangarorin biyu sun kafa tsarin abokantaka zuwa matsayin koli. Game da dimbin taimakon da kasar Sin ke baiwa Burundi kuwa, Karerwa ya ce, kasar Sin ta sha nanata matsayinta na nuna kin amince da duk wani kuduri da ya shafi nuna rashin adalci ga kasar Burundi. Ya ce a halin yanzu, suna goyon bayan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Burundi 100 bisa 100, kuma suna kara lalibo hanyoyin da za su kara kyautata mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu.

A cikin wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta karbi bakuncin taron dandalin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika wato FOCAC a birnin Beijing. Kakakin shugaban kasar ya ce, kasar Burundin za ta yi amfani da wannan dama na taron FOCAC wajen kara kyautata mu'amalarta da kasar Sin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China