in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da rijistar kuri'ar raba gardama da manyan zabukan Burundi a watan Fabrairu
2018-02-01 09:49:08 cri
Hukumar zaben kasar Burundi mai zaman kanta (CENI) ta sanya ranar 8 zuwa 17 ga watan Fabrairun wannan shekara, a matsayin ranakun da za a gudanar da rijistar kuri'ar raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar.

A baya dai an shirya gudanar da zaben raba gardaman ne a watan Mayu sai kuma manyan zabukan kasar da za su biyo baya a shekarar 2020.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar mai zaman kanta (CENI) Prosper Ntahorwamiye shi ne ya sanar da hakan, yana mai cewa, za a shafe kwanaki goma ne ana gudanar da wadannan ayyukan biyu a dukkan kauyukan kasar.

Ya ce za a fara aikin rijistar masu zabe ne da misali 7:30 na safe agogon kasar sannan a rufe da karfe 5:30 na yamma agogon kasar cikin wadannan kwanaki goma.

A cewarsa, su ma 'yan kasar dake zaune a kasashen ketare za su yi nasu rajistar ne a lokaci guda da takwarorinsu dake gida, sai dai za su yi nasu ne a ofisoshin jakadancin kasashen nasu.

Jami'in ya kuma bayyana cewa, sojoji da 'yan sandan kasar da ke aikin wanzar da zaman lafiya, musamman a Somaliya da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, su ma za su yi rajista a lokaci guda a wuraren da suke aiki, bisa sa-idon jami'in da hukumar za ta tura irin wadannan wurare.

A makon da ya gabata ne dai shugaban hukumar zaben kasar ta Burundi Claver Ndayicariye ya bayyana cewa, za a bude cibiyoyin yin rajista guda 3,828 a sassa daban-daban na kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China