Magufuli, wanda shi ne babban kwamandan askarawan kasar, yace wadanda suka kammala aikin yiwa kasa hidima kadai ne zasu cancanci samun guraben aikin a rundunar sojin kasar da ake saran dauka.
Shugaban ya bada sanarwar daukar sabbin jami'an ne a Arusha, a yayin da ya halarci bikin yaye kananan jami'an soji su 422 a kwalejin horas da jami'an soji ta Tanzaniya.
Yace baya ga guraben aikin da aka tanada a bangaran sojoji, har ila yau, gwamnatin kasar zata dauki sabbin ma'aikatan gwamnati kimanin dubu 50 cikin wannnan shekarar.
Samun karin guraben ayyukan, ya biyo bayan tantance ma'aikatan bogi da aka gudanar ne a kasar, da kuma bullo da shirin rage adadin kudaden da gwamnatin kasar ke kashewa, lamarin da ya sanya kasar ta samu rarar kudi kimanin dala miliyan 600.
Magufuli, ya jinjinawa rundunar sojin kasar a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasar har ma da kasashen waje inda dakarun kasar ke gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya.
Dakarun sojin kasar Tanzania suna bada taimako ga MDD wajen shiga shirin kiyayye zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo da Lebanon.