Kwamishinan Yankin Manyara Joel Bendera, ya ce gangamin ya shafi kowa da kowa, ciki har da wadanda ke zaune kusa da wuraren da aka kebe don yawon bude ido da shakatawa.
Ya ce abubuwan da gangamin ya kunsa sun hada da wayar da kai kan illolin dake tattare da safarar dabbobi ga rayuwar namun daji da kuma tattalin arzikin kasar. Ya ce masu safarar na fakewa da farauci kananan dabbobi da tsuntsaye, amma kuma manyan dabbobin dawa suke kashewa, yana mai cewa dalilin ke nan da ya sa suke kokarin rushe sana'ar.
Ya ce sun yi amana cewa, idan mutane suka ki saye tare da cin naman, masu safarar za su rasa kasuwa, abun da zai tilasta masu barin sana'ar. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin kananan hukumomi, don su hada hannu wajen yaki da cin namun daji ta hanyar bayyana sunayen wadanda ke da hannu cikin sana'ar.(Fa'iza Mustapha)