Sanarwar ta yi nuni da cewa, kanfan ruwan sama a lokacin damina ne ya sanya kasar ta Somaliya fadawa matsalar yunwa, lamarin da ya kara haifar da babbar barazana ga aikin samar da abinci a kasar. A hasashen da aka yi, 'yan kasar kimanin miliyan biyu da dubu 444 ke fuskantar matsalar rashin abinci, a yayin da wasu dubu 866 ke matukar bukatar taimakon abinci. Yawan mutanen da ke fama da yunwa a kasar ya karu da sau 10, bisa na shekarar bara
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, duk da cewa an dauki matakan yaki da bala'in yunwa a bara a kasar, amma jan aiki wajen kawar da matsalar kwata kwata daga kasar. Sanarwar ta kuma yi kira da a taimaka wajen inganta kwarewar kasar Somaliya ta fannin tinkarar yunwa a yayin da ake samar mata da taimakon jin kai. (Lubabatu)