Babban jami'in tawagar AMISON REX Dundun wanda ya sanar da hakan a jiya Lahadi, ya ce, za a tura jami'an 'yan sanda 40 daga kasashen Ghana, da Kenya, da Najeriya da Saliyo da Uganda da Zambia da suka kammala horon sanin makamar aiki zuwa ofisoshin 'yan sanda daban-daban dake Mogadishu, babban birnin Somaliya da kuma jihohin dake inuwar kungiyar AMISON.
A don haka jami'an tawagar 'yan sandan na AMISON, ya yi kira ga jami'an 'yan sandan da su gudanar da ayyukansu kamar yadda dokokin tawagar suka zayyana. (Ibrahim)