in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AMISOM ta ce karancin kudade na barazana ga aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia
2017-12-21 19:46:17 cri
Wakilin musamman na shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU a Somalia, kuma shugaban tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ko AMISOM a takaice, ya ce ayyukan tawagar da na dakarun tsaron kasar na fuskantar barazana sakamakon karancin kudade.

Mr. Francisco Madeira, ya ce AMISOM na bukatar tallafi domin aiwatar da kashin karshe, na matakan soja da ake dauka, don kwato sauran yankunan da a yanzu haka ke karkashin ikon kungiyar Al-Shabaab.

Jami'in ya ce tawagar AMISOM ta gaza cimma nasarar hakan ne, sakamakon karancin ma'aikata, da kalubalen tsare tsaren aiki da dai sauran su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China