in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An maida 'yan kasar Kamaru 72 gida daga Libya
2018-02-06 10:06:01 cri
An maida wasu 'yan ci rani 'yan kasar Kamasu su 72 gida, bayan da suka amince da hakan bisa radin kansu, karkashin shirin hukumar lura da bakin haure ta kasa da kasa IOM.

A ranar Litinin ne dai aka kwashe mutanen su 72 daga wani sansanin killace bakin haure da suka shiga Libiya ba bisa ka'ida ba, aka kuma mayar da su Kamaru bisa kulawar jami'an hukumar ta IOM.

Wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida da hana zirga zirga ba bisa ka'ida ba ta kasar Libiya ta fitar, ta ce wadanda aka mayar Kamarun sun hada da mata da yara kanana. An kuma kwashe mutanen ne ta filin jiragen sama na M'etiga dake birnin Tiripoli.

Kasar Libiya dai ta kasance zango da 'yan ci rani masu nufin shiga Turai ke fakewa, a hanyarsu ta shiga kasashen na Turai ta tekun Meditireniya. Ana kuma alakanta hakan da yanayin karancin tsaro, da danbarwar siyasa da ke addabar kasar, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Gaddafi a shekarar 2011.

Akwai dai dubban bakin haure dake zaune a Libiya, ciki hadda wadanda aka ceto ko wadanda jami'an tsaron kasar ke tsare da su, kuma hukumar IOM na samar da dama ta mayar da su gida idan har sun amince da hakan.

An fara aiwatar da wannan shiri ne na IOM a shekarar 2006, kuma a shekarar 2017 kadai, an mayar da bakin haure da yawansu ya kai 20,000 zuwa kasashen su na asali. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China