MDD: Mai yiwuwa mutane 90 sun hallaka sakamakon nutsewar wani kwale kwale a gabar ruwan Libiya
Hukuma mai kula da harkokin bakin haure ta MDD, ta ce mai yiwuwa ne wasu 'yan cin rani da yawan su ya kai 90 sun hallaka, bayan da kwale kwalen da suke ciki ya nutse a gabar ruwan kasar Libiya da sanyin safiyar Juma'ar nan.