in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya zai ceto tattalin arzikin Libya daga durkushewa
2018-02-04 12:26:47 cri
Wani mamba a majalisar wakilai dake gabashin Libya, Tariq Al-Jarushi, ya bayyana cewa, tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya zai taimakawa tattalin arzikin Libya wajen kaucewa fuskantar gibi.

Al-Jarushi, ya fada cikin wata sanarwa cewa, idan farashin danyen mai ya tashi, zai ceto kasar ta Libya daga fuskantar komadar tattalin arziki da samun nakasu. Bayan tsakiyar shekarar 2018, fasahin danyen man kasar ta Libya zai iya kaiwa dalar Amurka 90 kan kowace gangar danyen mai.

Sai dai ya bayyana fargaba sakamakon matsin lambar kasa da kasa, wanda hakan zai iya haifar da karuwar hare haren kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai da na kungiyoyin ta'addanci wanda hakan zai iya hana kamfanonin dake aikin hakar danyen man kasar ta Libya ci gaba da ayyukansu.

Al-Jarushi ya ce, alamu sun nuna cewa tattalin arzikin Libyan yana farfadowa. Sai dai a cewarsa akwai kasashen duniya dake son tsawaita tabarbarewar al'amurran tattalin arziki da na tsaro a Libyan. Suna ta kokarin ingiza kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC, na neman ta takaita tashin farashin danyen mai na kasar Libya.

Cikin shekaru hudun da suka gabata, kasar Libya ta tafka hasarar sama da dala biliyan 140, a sakamakon ci gaba da rufe rijiyoyin mai da tashoshin ruwan kasar, saboda hare-haren 'yan ta da kayar baya da kuma faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China