in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsawaita rajistar katin zabe na babban zaben kasar Libya dake tafe zuwa tsakiyar watan Fabrairu
2018-02-02 10:58:14 cri
Babbar hukumar zaben kasar Libya ta sanar da tsawaita wa'adin rajistar bada katin zabe na babban zaben kasar dake tafe har zuwa tsakiyar wannan watan na Fabrairu.

Shugaban hukumar zaben na Libya Imad Sayeh, ya fadawa taron manema labarai a Tripoli babban birnin kasar cewa, an samu karuwar masu yin rajistar katin zaben ne sakamakon wayar da kan jama'a da aka dinga gudanarwa game da muhimmancin dake tattare da shiga harkokin zabe a matsayin wani muhimmin jigon kafa tsarin demokaradiyya don zabar shugabannin da mutane suke son su jagorance su.

Sayeh ya kara da cewa, don haka suka yanke shawarar tsawaita wa'adin yin rajistar masu zaben har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, domin bayar da babbar dama ga mutanen da ba su samu damar yankar katin zaben ba, a babban zaben kasar mai cike da tarihi wanda za'a gudanar a nan gaba.

A bisa ga alkaluman kididdiga da hukumar ta fitar, mutane 2,267,000 tuni sun riga sun yi rajistar katin zaben.

A ranar 6 ga watan Disambar shekarar 2017 ne, hukumar zaben kasar ta fara aikin yin rajistar masu kada kuri'ar na tsawon watanni biyu a duk fadin kasar ta Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China