Wakiliyar IOM a kasar Libiya Olivia Headon, ta ce an samu gawawwakin wasu mutum 10 da ruwa ya turo bakin gabar tekun, ciki hadda na 'yan Libiya 2 da kuma wasu 'yan kasar Pakistan su 8.
Madam. Headon ta ce akwai kuma wasu mutum biyu da suka tsira bayan da suka yi iyo zuwa bakin gabar ruwan, yayin da wani kuma masunta suka ceto su da jiragen su na kamun kifi.
Hukumar IOM ta ce tana ci gaba da bincike, domin samun cikakkun bayanai game da aukuwar hadarin, tare da duba yiwuwar tallafawa wadanda suka tsira.