Wani sojan dake aiki a runduna ta 12 ta sojojin kasar Mohamed Magrahi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Laraba cewa, an kashe mayakan na IS guda biyu ne a wani bata kashi tsakanin mayakan da sojojin rundunar da kuma mazauna birnin. Sojojin dai sun tunkari wasu mutane uku ne da suka zo sayan kaya a wani shago dake yankin domin su bayyana kansu, amma daga bisani sai suka fara nuna shakku a kan mutanen, daga nan ne mutanen da ake zargi suka harbe wani soja har lahira kafin daga bisani su gudu da motarsu.
Magrahi ya ce, ana haka ne kuma sai wani soja da wasu matasan birnin suka budewa mutanen da ake zargin 'yan ta'adda ne wuta, inda suka fafare su har zuwa inda motarsa ta lalace. Daga bisani an samu biyu daga cikin mutanen a mace a wajen birnin.
Mayakan IS dai na yawan kai koma tsakanin wajen birnin dake kudancin kasar, inda suke amfani da yanayin hamadar da ta tsara yankin suna kaddamar da munanan ayyuka. (Ibrahim Yaya)