in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin: Ya kamata a yi la'akari da batun sake gina kasar Sham bayan yaki
2017-10-16 13:27:27 cri

A kwanakin baya ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi jawabi a yayin bikin bude babban taro karo na 137 na majalisun dokoki na kasa da kasa, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su yi la'akari da batun sake gina kasar Sham bayan yaki.

Shugaba Putin ya kuma nuna cewa, bai kamata ba a dauki ma'aunai biyu kan batun yaki da ta'addanci, kuma bai dace a alakanta da batun da muradun siyasa ba. Ya kamata bangarori daban daban su inganta hadin kan dake tsakaninsu, a kokarin kau da ta'addanci. A cewarsa, ko wace kasa na da ikon zabar hanyar raya kanta. Muddin aka tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa ba tare da la'akari da yanayinta na musamman ba, hakika za a ta da hankali a wurin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China