in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da MDD sun yi Allah wadai game da wargaza yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta kudu
2018-01-13 12:53:02 cri
Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU da MDD, sun yi Allah wadai da babbar murya game da saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna a Sudan ta kudu.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin shugaban kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, sun yi Allah wadai game da wargaza yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba hannu kanta a ranar 21 ga watan Disambar 2017, wadda ta shafi batun tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin dake rikici da juna a Sudan ta kudu, domin a samu damar bada kariyar ga fararen hula da samar da kayayyakin jin kai ga al'ummomin kasar dake bukatar taimakon gaggawa.

Jami'an biyu sun bukaci sassan dake yaki da juna a Sudan ta kudu da su kai zuciya nesa, kuma su guji daukar duk wani matakin soji, kana su dawo kan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka riga aka cimma matsaya kanta a ranar 21 ga watan Disambar shekarar 2017.

Sanarwar ta kara da cewa, an bukaci bangarorin da su yi kokarin sauke nauyin dake wuyansu na kare lafiyar fararen hula, kuma su mutunta dokokin hakkin dan adam na kasa da kasa, da dokokin bada jin kai na kasa da kasa, kuma su tabbatar an samu damar shigar da kayayyakin jin kai a yankunan dake bukatar tallafi ba tare da wata tangarda ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China