Mr. Ateny ya ce sun samu shaidu dake nuna cewa, tsakanin ranekun 26 zuwa 28 ga watan Disambar bara, tsohon janar din ya umarci masu yi masa biyayya da su kai hari kan garuruwan Aweil da Wau. Kaza lika ana zargin sa da kitsa tashin hankalin da ya auku cikin makon jiya a kusa da birnin Juba.
Gwamnatin Sudan ta Kudun dai ta ce ta samu wasu bayanan sirri na murya da aka nada, masu tabbatar da zargin da ake yiwa janar din, inda yake magana da yaren Dinka, ko da yake dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tantance sahihancin wannan sauti na murya. (Saminu Hassan)