Kamfanin dillancin labarai na kasar Libya ya ruwaito cewa, mota ta farko ta fashe a gaban wani masallaci dake unguwar Salmani ta garin Benghazi, a lokacin da mutane da yawa suke addu'a a cikin masallacin. Sa'an nan, bayan da motar asibiti ta isa wuri don ceton wadanda suka jikkata, mota ta 2 ta kara fashewa, lamarin da ya haddasa rasa rayukan karin mutane masu yawa.
A cewar Fadia Al-Barghathi, kakakin asibitin Al-Jalaa na garin Benghazi, a kalla wasu mutane 22 sun rasa rayukansu, yayin da sauran 21 suka jikkata. Sai dai jimillar ba ta shafi mutanen da aka garzaya da su sauran asibitoci ba.
Hare-haren wannan karo sun kasance mafiya muni cikin watannin da suka gabata. Zuwa yanzu babu mutum ko wata kungiya da ta fito fili ta dauki alhakin kaddamar hare-haren.(Bello Wang)