Yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar MDD dake birnin New York, Guterres ya ce, bangarori daban-daban dake halartar shawarwarin sun amince da kafa kwamitin tsara kundin tsarin mulki na Siriya karkashin jagorancin MDD, kana, a wajen shawarwarin shimfida zaman lafiya kan batun Siriya da MDD zata jagoranta a birnin Geneva, za'a tabbatar da nadin membobin kwamitin, da ayyukansu, da manufofin kwamitin da sauransu.
Antonio Guterres yana mai cewa, wakili na musamman na babban sakataren MDD kan batun Siriya, Staffan de Mistura, aikinsa a nan gaba shi ne, tabbatar da aiwatar da kudurorin da kwamitin sulhun MDD ya amince da su daga dukkan fannoni.
Domin taimakawa ga wanzar da zaman lafiya a kasar Siriya, wasu kasashe uku, ciki har da Rasha da Turkiyya da Iran sun bada shawarar kaddamar da shawarwari kan batun Siriya. An rufe shawarwarin a daren ranar 30 ga watan Janairun bana a birnin Sochin dake kudancin kasar Rasha, inda mahalarta taron suka bullo da hadaddiyar sanarwa, don yanke shawarar kafa kwamitin shirya kundin tsarin mulki na Siriya.(Murtala Zhang)