in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ta yaba da tattaunawar Sochi a matsayin matakin farko na kawo karshen rikicin siyasar kasar
2018-02-02 10:38:32 cri

A jiya Alhamis gwamnatin kasar Syria ta ce ta yi na'am da sakamakon da aka samu na tattaunawar da kasar Rasha ta jagoranta a Sochi game da batun zaman lafiyar kasar ta Syria, inda tace hakan ya kasance a matsayin matakin farko na warware rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar, inji kamfanin dillancin labaran Syriar SANA.

An shirya babban taron tattauna batun rikicin Syriar ne a birnin Sochi tsakanin ranakun 29 da 30 ga watan Janairu, inda Rasha ta gayyaci mutane 1,600 don halartar taron, kuma wannan shi ne taro mafi girma da aka shirya don tattauna batun zaman lafiyar Syria.

An karkare taron ne inda aka fidda sanarwa wadda ta amince da cimma yarjejeniyar kafa kwamitin da zai yi nazari kan dokokin mulkin kasar, wanda ya kunshi mutane 150 daga bangarorin 'yan adawa da na gwamnatin kasar, wanda zai tattauna yadda za'a yiwa kundin tsarin mulkin kasar na yanzu gyaran fuska, a maimakon tsara wani sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Sanarwar ta ayyana bukatar kafa tsarin hada kan yankunan kasar ta Syria, ba tare da tunbuke shugaban kasar Bashar al-Assad daga mukaminsa ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China