in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin gwamnatin Syria na adawa da shirin sulhuntawa da kasashe biyar suka gabatar
2018-01-28 13:29:42 cri
Shugaban tawagar wakilan gwamnatin kasar Syria, kuma wakilin dindindin na kasar dake MDD Bashar al-Jaafari ya ce, gwamnatin kasarsa na adawa da shirin sulhunta rikicin kasar da kasashe biyar suka gabatar, ciki har da Amurka da Saudiyya.

Bashar al-Jaafari, ya bayyana haka ne a ranar 26 ga wata a yayin da yake halartar shawarwarin zaman lafiyar Syria na sabon zagaye wanda ke gudana a halin yanzu a Vienna.

Kafin hakan, kasashe biyar da suka hada da Amurka, Burtaniya, Faransa, Saudiyya da kuma Jordan, sun gabatar da wata takarda ga De Mistura, manzon musamman na babban sakataren MDD, inda suka bukaci a gabatar da wasu batutuwa a yayin wannan shawarwarin zaman lafiya, ciki har da tattaunawa kan yin kwaskwarimar tsarin siyasar Syria ba tare da bata lokaci ba, da kuma hakikanan shirin shirya zabe cikin 'yanci a fili. Game da wannan, Bashar al-Jaafari ya bayar da sanarwa cewa, gwamnatin kasar Syria na adawa da duk abubuwan dake cikin takardar, jama'ar kasar ma ba zasu amince dasu ba. Kana wakilin ya ce, gwamnatin Syria ta amince da babban taron tattaunawar kasar bisa shawarar kasashen Rasha, Turkiyya da kuma Iran, za ta halarci taron.

Amma a nasu bangare dakarun dake adawa da gwamnatin Syria sun ki halartar taron.

A ranar 27 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova ya ce, wakilan Kurdawa na Syria za su halarci wannan taron da za a shirya a tsakanin ranar 29 zuwa 30 ga wata a birnin Sochi na kasar Rasha. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China