in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Turkiya sun shiga kasar Syria
2018-01-22 13:07:40 cri
Firaministan kasar Turkiya, Binali Yildirim, ya sanar a jiya Lahadi cewa, sojojin kasar sun riga sun shiga cikin kasar Syria, inda suka fara daukar matakai a yankin Afrin dake arewacin kasar.

Jami'in ya yi furucin ne a birnin Istanbul, inda ya ce sojojin kasar Turkiyya na gudanar da wannan matakin ne da hadin gwiwar dakarun 'yan adawa na kasar Syria ko "Sojojin 'yantar da Syria", matakin da ya nuna an fara kaddamar da matakan soja ta kasa.

A cewar mista Yildirim, matakin sojan na da nufin dakile sojojin Kurdawa, kuma ana sa ran kammala matakin cikin sauri. Daga bisani za a kafa wani yanki mai tsaro, wanda fadinsa zai kai kilomita 30 cikin yankin Afrin. Jami'in ya nanata cewa, ana gudanar da matakin sojan ne domin dakile ayyukan 'yan ta'adda, maimakon azabtar da fararen hula.

Kafin hakan, wani gidan telabijin na kasar Turkiya ya ba da labarin cewa, wasu rokokin da aka harba daga kasar Syria sun dira garin Reyhanli na Turkiya, wanda ke dab da kan iyakar kasa, tare da haddasa mutuwar wani mutum, gami da jikkata wasu 32.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China