in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta horas da 'yan sandan Somaliya fasahar kwance boma bomai
2017-12-18 09:59:17 cri
Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM) a ranar Lahadi suka kammala wani shirin ba da horo na kwanaki 10 wanda aka shirya da nufin koyar da dabarun yadda za'a magance saurin yaduwar boma bomai da ake fama da shi a kasar.

Shirin ba da horon wanda aka shiryawa 'yan sandan jihar South West ta kasar, an gudanar da shi ne a birnin Baidoa dake kudancin Somaliya, wanda ya mayar da hankali kan rigakafi da kuma gano abubuwan fashewa da aka daddasa, wanda mayakan kungiyar Al-Shabaab dake Somaliya suka mayar da amfani da boma boman a matsayin babban makaminsu mafi girma da suke amfani da shi wajen kaddamar da hare hare.

Jami'i mai kula da 'yan sandan AMISOM, Sahr Emmanuel Kobai-Aruna, ya bayyana a lokacin bikin kammala shirin ba da horon cewa, an tsara shirin ne da nufin samar da kwarewa ga 'yan sandan jihar South West, kuma an baiwa jami'an horo ta hanyar ilmantar da su darrusa masu yawa game da daukar matakan kariya da tabbatar da tsaro.

Kobai-Aruna ya bayyana cikin wata sanarwa bayan kammala shirin bada horon cewa, wannan yana daya daga cikin manufofin AMISOM na kokarin horas da jami'an 'yan sandan Somaliya, da kuma horas da su game da dabarun yadda ake ganowa da kwance ababen fashewa, da kuma sauran batutuwa da suka shafi gudanar da aikin tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China