in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RBDA da kamfanin kasar Sin sun kulla yarjejeniyar noman rogo
2018-02-01 09:23:01 cri
Hukumar raya kogin jihar Cross Rivers dake yankin kudu maso gabashin Najeriya ta kulla wata yarjejeniyar bunkasa noman Rogo da rukunin kamfanin kasar Sin mai suna Ruyi Holding Group.

Da yake karin haske game da hakan, manajan darektan hukumar RBDA Bassey Nkposing ya ce yarjejeniyar za kuma ta kunshi gina tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa a yankin, da yin hadin gwiwa tsakanin manoma da matasa gami da 'yan kasuwan dake yankin, inda ake fatan sama da iyalai manoma 1,000 dake yankin za su shiga cikin wannan shiri.

Nkposong ya ce, hukumar tana maraba da zuwan kamfanin na kasar Sin, kana a shirye take ta kara marabtar masu sha'awar zuba jari a bangaren albarkatun noman yankin.

A nasa jawabin shugaban tawagar kamfanin na kasar Sin Wang Wei, ya ce, akwai bukatar a kara noma albarkatun gonan dake yankin. Yana mai cewa, kamfanin zai yi kokarin cin gajiyar tashar samar da wutar lantarki dake madatsar ruwan Ijegu Yala, ta yadda za a kai hasken wutar lantarki yankin da kamfanin zai gudanar da wannan gagarumin aiki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China