Jami'in ya yi wannan furuci ne bayan wani rangadin da ya kammala a tsibirin Lekki a Jumma'ar da ta gabata, inda ya kara da cewa, hukumomin kasar za su samu kudin da ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 201 daga harajin da za a tara kan ayyukan da za a gudanar a tashar jiragen ruwan. Ban da haka, tashar jiragen ruwa za ta baiwa yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki damar samun karin guraben ayyukan yi fiye da dubu 170, inda yawan kudin albashin da ma'aikatan tashar za su samu zai kai kimanin dalar Amurka biliyan 20.
Bisa shirin da aka yi, tashar jiragen ruwa ta Lekki za ta kasance a tsakiyar yankin ciniki cikin 'yanci na Lagos, kuma za ta taimaka wajen raya tattalin arzikin kasar Najeriya da tallafawa harkokin cinikayya a daukacin yankin yammacin Afirka, gami da zama wata babbar cibiyar jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa ta kasa da kasa.(Bello Wang)