Birgediya janar Bello Mohammed, shi ne kwamandan runduna ta 23 ta sojojin kasar ya tabbatar da hakan ga 'yan jaridu a Yola, babban birnin jihar ta Adamawa, ya ce daga cikin wadanda aka damke har da wani hakimi.
Mohammed ya ce, dakarun sojin kasar suna cigaba da gudanar da bincike don gano sojan da ya bace.
A wani labarin kuma, mazauna kauyen na Opallo sun fara tsarewa saboda fargaba, inda wasu ke zargin cewa sojoji sun cinna wuta a wasu sassa na kauyen.(Ahmad Fagam)