in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar harin da aka kai kwalejin horas da 'yan sanda na Somalia ya karu zuwa 18
2017-12-15 13:53:44 cri

A kalla jami'ai 18 ne suka mutu, wasu 15 suka jikkata, yayin wani harin kunar bakin wake da aka kai Kwalejin horas da 'yan sanda dake Mogadishu babban birnin Somalia da safiyar jiya Alhamis.

Dan kunar bakin waken ya ta da bam din dake jikinsa ne a daidai lokacin da jami'an ke karin kumallo, sabannin rahotannin da aka bayar a baya dake cewa jami'an na fareti a lokacin da harin ya auku.

Mukaddashin shugaban 'yan sanda Mukhtar Hussaein Afrah, ya shaidawa manema labarai cewa, maharin na sanye da kayan 'yan sanda kuma ya tada bam din ne a lokacin da jami'ai ke karin kumallo.

Abdullahi Hamud, karamin minista a ofishin Firaministan kasar, ya tabbatar da cewa 'yan sanda sun gano maharin kuma za su fitar da bayanansa bayan sun kammala bincike.

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, wanda ya zo watanni 2 bayan harin da aka kai cikin babbar mota kan wani waje mai yawan hada-hadar jama'a a ranar 14 ga watan Oktoba, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 512 tare da jikkata wasu sama da 300. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China