in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somaliya, AU da MDD za su nazarci matakan tabbatar da tsaron Somaliya
2017-12-04 10:11:22 cri
Kasar Somaliya za ta karbi bakuncin babban taro kan al'amuran tsaro domin neman tallafi game da yadda za'a shawo kan matsalar tsaron kasar gabanin ficewar dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika daga kasar.

Taron wanda shirin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM) ya shirya, tare da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, zai mayar da hankali ne wajen tattauna hanyoyin da za'a samar da kudade ga hukumomin tsaron kasar Somaliya da kuma nazari kan matakai na gaba da za'a dauka game da shirin na AMISOM.

A wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu, wakilin musamman na shugaban kungiyar AU dake Somaliya Francisco Caetano Madeira ya bayyana cewa, taron yana da matukar muhimmanci wajen duba irin nasarorin da aka cimma a halin yanzu dangane da batun tsaro da rikicin siyasar kasar Somaliya.

Madeira ya ce, za'a auna irin nasarorin da aka samu da kuma duba irin matakan da za'a dauka a nan gaba wanda zai baiwa AMISOM damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, da kwararan matakan da za'a dauka wajen murkushe kungiyar al-Shabaab. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China