in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Mali hudu sun mutu a sakamakon harin kunar bakin wake
2018-01-29 13:27:59 cri
Rahotanni daga Mali na cewa sojojin kasar hudu suka mutu a sakamakon wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai a arewacin kasar.

Sanarwar ta rudunar sojan kasar ta fitar ta bayyana cewa, wani mutum ne ya kai harin bam din kunar bakin waken, inda ya yi yunkurin kai hari kan watar cibiyarr binciken ababan hawa ta soja dake birnin Menaka a arewacin kasar Mali a wannan rana da safe, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar guda hudu yayin da suke kokarin hana shi tayar da bam din.

Daga watan Janairu na bana, an kai hare-hare da dama baya ga wasu bama-bamai da suka fashe a kasar ta Mali. Ko da a ranar 11 ga wata ma sojojin kasar Faransa 3 suka ji rauni a sakamakon wani harin bam da aka adana a cikin wata mota a gabashin kasar Mali. Haka kuma a ranar 25 ga wata, wata motar bas ta taka wata nakiya yayin da take kan hanyar zuwa Mali daga Burkina Faso, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 26 tare da raunatar wasu da dama. A ranar 27 ga wata, wasu dakaru sun kai hari kan wani sansanin soja dake arewacin kasar Mali, harin nan ma ya haddasa mutuwar sojoji a kalla 16 tare da raunata fiye da mutane 10. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China