in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai Mali
2018-01-27 17:01:00 cri
Jiya Jumma'a, kwamitin tsaron MDD ya fidda wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai kasar Mali, kana ya nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma mika sakon ta'aziyya ga gwamnatocin kasar Mali da kasar Burkina Faso.

A ranar 25 ga wata, wata motar bus wanda ta taso daga kasar Burkina Faso ta tarwatse a tsakiyar kasar Mali, sakamakon taka boma-bomai, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 26, yayin da wasu suka jikkata, cikin wadanda suka rasu har da wasu 'yan kasar Burkina Faso.

A sanarwar da kwamitin MDD ya fitar, ya nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Mali wajen yaki da ta'addanci, haka kuma kwamitin ya jaddada muhimmancin kara karfin yaki da ta'addancin a yankunan kasar baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China