in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya bukaci bangarorin Mali da su yi kokarin tabbatar da zaman lafiya
2017-10-06 12:24:01 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci sassa masu ruwa da tsaki na kasar Mali da su hada kai don ganin sun tabbatar da zaman lafiya a kasar, bayan da turkaturkar siyasar kasar a 'yan watannin da suka gabata ta kusa kawo cikas ga kokarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma.

Jadakan kasar Faransa a MDD Francois Delattre, kana shugaban kwamitin sulhu na wannan wata, ya ce kwamitin sulhun ya yarda da aikewa da sako mai karfi ga bangarorin kasar ta Mali, kana ya amince ya yi kokarin ganin ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Mali da kuma sabuwar rundunar sojojin hadin gwiwa ta kasashe biyar da aka kafa a yankin suna gudanar da ayyukansu kamar yadda aka tsara.

Shi ma wakilin musamman na babban sakataren MDD kan batun kasar Mali Mahamat Annadif, ya shaidawa kwamitin sulhu cewa, a 'yan watanni da suka gabata, mawahawar da ake yi game da yiwa kundin tsarin mulkin kasar Mali gyaran fuska, da rikici tsakanin jagororin da suka sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, sun kusa kawo nakasu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma.

Ya kuma yi gargadin cewa, tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali tana fuskantar manyan kalubaloli masu nasaba da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin 'yan ta'adda da sauran bata gari.

A don haka ya yi kiran da a kare lafiyar masu aikin wanzar da zaman lafiya dake kasar ta Mali, ganin yadda dakarun ke rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu. Ya ce yanzu haka, kaso 35 cikin 100 ne kawai na ayyukan jin kai da aka tsara ake daukar nauyin su. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China