in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali ta yabawa Algeriya kan rawar da take takawa game da zaman lafiyarta
2018-01-14 13:20:13 cri
Firaministan Mali Soumeylou Boubeye Maiga, wanda ke ziyarar aiki a kasar Algeriya ya yabawa kasar bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da zaman lafiyar Mali.

Maiga ya fadawa 'yan jaridu a yayin ziyarar aikin ta kwanaki biyu da ya kai kasar ta arewacin Afrika cewa, a ko da yaushe kasar Algeriya tana taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiyar Mali, kana ta taimaka wajen kaiwa kasar dauki har sau biyu ta hanyar kafa kwamitin tattaunawar zaman lafiyar kasar Mali a shekarun 1992 da 2015.

Ya ce babban ginshikin da kasar Mali take amfani da shi wajen tabbatar da zaman lafiya da cimma daidaito na cikin gida da na kasa da kasa ya samo asali ne kan shirin zaman lafiyar da aka bullo dashi wanda kasar Algeriya ta kasance jigo.

Ya kara da cewa, kyakkyawar mu'amalar dake tsakanin Mali da Algeria yana da dadadden tarihi, ya kara da cewa, makasudin ziyarar aikin da ya ya kai shi ne don kyautata mu'amalar dake tsakanin bangarorin biyu a dukkan fannoni. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China