Babban sakataren MDD Antonio Guterres da kwamitin sulhun MDD sun yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kaiwa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya dake Mali.
Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa ya rabawa maname labarai, ya nanata cewa, duk wani hari kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD tamkar aikata manyan laifuffuka karkashin dokokin kasa da kasa, don haka ya yi kira ga mahukuntan Mali da su gaggauta zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki da nufin hukunta su.
Bugu da kari, Mr Gutterres ya bukaci gwamnatin Mali da kungiyoyi masu dauke da makamai da su yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da suka amince da suka sanya hannu, kana su tabbatar da cewa, irin wadannan hare-hare ba su kawo nakasu ga kokarin da MDD ke yi na taimakawa kokarin al'ummar Mali na samar da zaman lafiya a kasar ba.
Sojojin kasar Chadi uku ne suka rasa rayukansu kana wasu biyu kuma suka jikkata bayan suka taka wata nakiya a jiya Alhamis, yayin da suke yiwa wani ayari rakiya a arewacin Mali.(Ibrahim)